ILLOLIN DAKE TATTARE DA SANYA HOTO GA 'YA MACE A SOCIAL MEDIA
'YAN'UWA MATA MATSO KUSA KUJI!!!
Kuna chatting da Budurwarka a tsakiyar dare. Nan take sai sha'awarka ta motsa Sai kayi maza ka nemi ta turo maka nude pics, Taƙi amincewa da hakan tace a'a plsss Kayi hakuri
Kaci gaba da mata magiya ta nemi ka fahimceta akan bazata iyaba Kace mata ta aminta dakai ta kuma yarda akan bazaka bar kowa ya gani ba, Tace maka bazata iya nuna jikinta ga kowa ba idan ba mijin daya aure ta ba
Kaci gaba da magiya Daga bisani tace ka dan jirata kaɗan Kayi haƙuri ka tsaya jiranta Ta daure ta turo maka, kayi farin ciki da hakan Ka kalla har ka ɓata jikinka, Ka sake kallon nude pics din sai kaji yana baka haushi,
Sai kayi tunanin abun yayi muni bayan ka gama Istimna'i daka kalli pics din Sai ka hau kan Facebook ka tafi mobile upload, Ka upload na pics ɗin da wani rubutu a kasansu harma kayi tag ɗinta a jiki.
Tana kuka ta maka message ta inbox tana roƙon ka ka goge amma kayi kunnen Uwar shegu kaƙi Gogewa Tace maka zata turo maka wassu dayawa idan har ka goge, Kace mata kaga duk abinda kake buƙata.
Facebook Friends naka suka fara Likes da Maganganu akan nude pics din nata Wasu suna zaginta Wasu suna cewa baka kyauta ba, Wasu suna yabon surarta, Wasu suna bata kariya akan abinda ka mata, Wasu kuma suna Dariya
Ƙawayenta suka ga nude pics din, Wasu sun zageta Wasu kuma sun ji takaicin faruwar hakan, Wasu sun bata kariya, amma hakan bai amfanar da ita komai ba domin dayawa sunga pics din.
Wasu sunyi Sharing na pics din zuwa Wasu Groups, Wasu sunyi Saving a Wayoyin su, Wasu kuma danginta suka kaiwa pics suka nunawa, Tayi dana sanin Saninka da tayi, tayi nadamar abinda ta aikata , tayi kuka iya Kuka
Washe gari ta tafi school. Ta gamu da Wasu Ƙawayenta suna mata Ihu, Ta shiga aji, tana ƙoƙarin zama kawai sai ga Head Teacher nasu yayi Kiranta.
Head Teacher ɗin ya sanyata Explaining meye yafaru abinda yakeji kuma ya gani? Ta kasa bayanin komai . Aka mata duka kamar jaka. Malamin ya kira iyayenta Sukayi magana da Head Teacher ɗin, daga bisani dai sai akace an koreta a makarantar gaba ɗaya.
Iyayen nata sukayi kaɗawar Duniya Head Teacher yayi haƙuri Amma yaƙi saboda taurin Xuciya, Ta dawo gida, iyayenta abun yabasu kunya, suma suka Jibga mata uban duka kamar jaka.
Suka kwace wayarta Rayuwarta ta susuce tashiga kunci da bakin ciki, Tayi ƙoƙarin mantawa da abun da yafaru domin cigaba da Rayuwarta, amma duk inda ta fita sai ana nunata da yatsa,
Kowa wai sai dai taji suna magana a kanta
Wasu suna mata Dadariya Ta dawo gida Tunani yayi mata yawa, Sai ta yanke hukuncin Aiwatarwa kanta kisan kai ko tasamu Sauqi
Tashiga dakin mahaifiyarta Tasamo maganin ɓera, Tayi maza ta sha maganin ɓeran Cikin Mintuna biyu tace ga garinku, Iyayenta sukaji shiru Suka ƙwala mata ƙira Bata amsa ba
Ransu ya sake ɓaci suka kara ƙwala mata ƙira nanma bata amsa ba. Sai suka fusata suka nufi Dakinta domin su Duba Sai suka tarar ta Mutu ga Maganin ɓera a gefenta
Suka ɗimauce suka ji bakin ciki, suka daurawa kansu alhakin abinda ta aikata. Sukayi kuka sukayi dana-sanin hukuncin da sukayi mata, Suka ƙirayi danginta da ƙawayenta na kusa.
Kowa yasan abinda ya faru sukaji bakin ciki, Ƙawayenta na ƙud-da-ƙud suka sha kuka kamar ba gobe domin basu yarda ta mutu ba
Shi wannan wanda ya yaɗa nude Pics dinta yaji labarin, Ranshi yaji yayi baƙi rayuwarsa tayi Masa zafi, Yayi dana sanin abinda ya aikata yana inama hannun agogo zai koma baya!
Aka shirya mata janaza, Ƙawayenta da iyayenta suka zo kusa da gawar nata ana ƙoƙarin fita da ita, duk suka fashe da kuka. Kowane na kusa da ita jikinsu a mace domin ta tafi ta barsu
.....................
Abun yafara kamar da Sauƙi da wasa wanda daga bisani kuma ya rikice, Yan'uwa masu hankali da tunani mu sani cewa zamu iya wargaza Rayuwar wani a Ƙanƙanin lokaci akan wani abinda mukaga bai kai Komai ba.
Mu dinga sara muna duban bakin gatari Yan'uwa masu hankali da tunani musamman mata, ku kiyaye mutuncinku kuna tsare kawunanku daga samarin banza hadda ma ko Wasu irin samarine matuƙar zasu nemi ganin pics naku a wani yanayi wanda bai dace ba ..
Dan'uwa ka sani duk wanda zai aikata wani abun ƙi tsakanin shi da wata sannan yazo yana nunawa ko shaida wa yayi, wannan tubar shi tana wahala
Allah muke roƙo Ya karawa rayuwarmu albarka Ya kuma shiryar damu hanyar da ta dace. 'Yam mata sai a Kula da Irin wadannan Samari.