SHAWARA ZUWA GA MA'AURATA MASU HUSUMA DA MASU NIYAN AURE
Babu Shakkah da yawa daga cikin Ma'aurta suna samun husuma a gidan auren su saboda rashin aiwatar da wasu muhimman abubuwa a zaman takewar su, kafin nayi baya nin wayannan abubuwa Farko fari kamata yayi ma'aurata su san hakkokin da ke kansu, su fahimci mene ne sharia ta dora akansu tun gabanin akai ga zamantake war Auren. Wadda In shaa Allahu zan yi kokarin Zakulo wayannan Hakkoki domin dukan mu ma amfana dasu. A rubutu nagaba
Lallai ya kamata Ma'aurata su sani bazasu taɓa samun nasara da rabauta ba a cikin gidansu har sai sunyi riko da wassu sifofi guda goma da zasu rika bada su ga junansu, kana suna mai kwadayin aiki da su da kiyaye su;
Zan fara da Maza kafin na lissafo na mata
ABINDA YAKAMATA MAZAJE SU SANI A ZAMAN TAKEWAR AURE
NA FARKO DANA BIYU, Ka sani! lallai dukkan mata suna son a shagwaba su, suna kuma son a rinka bayyana musu ana son su cikin lafazi karara, Kada ka yadda ka yi rowar abubuwan nan guda biyu ga matakarka, in kuma ka kuskura ka hana mata su, to hakika ka sanya shamakin nisantawa ne tsakaninka da ita, tare da kawo tasgaro da karanta soyayya".
Ga Tambaya Ga mazanmu ma'aurata, Shin daga cikin mu sau nawa muke kiran matayen mu, mu furta musu "I love you?" bayan mun fita kasuwa ko Ofis?
Shin daga Cikin mu Sau nawa Muka shirya zamu fita kasuwa ko Ofis, mu cewa, matar mu, mun fasa fita yau, mun bata gaba dayan yinin yau?
Babu shakkah yanda duk kake so a nuna maka so da kauna to macce ta fika son haka ninkin ba ninkin. Don haka mu kula.
NA UKU KUMA: Ka sani! Lallai su mata suna kin mutumin da keda tsanani, da hazama, (wanda baya sassautawa, ko-yaushe), suna kuma neman hidimtawar namiji mai rauni da
tausayi, Yi kokarin sanya kowacce sifa a gurbinta, don yin hakan ne kawai zai jawo muku soyayya, tare da samar da
nitsuwa!".
Babu shakkah daga cikin mazajen mu a yau ba sa da hankuri da macce ta musu abu kadan sai fada, hakika mata basa son haka, don haka kada ka kuskura ka rika mata fada akan duk abinda ta yi, ka zama mai yafiya a garesu. Mata suna son haka.
ABU NA HUDU KUMA: Ka Sani cewa mata suma suna so daga mazajensu irin abinda miji ke so daga gare su; na daddadar magana, da cancada ado, da tsaftace tufa, da kuma tashin kamshi, Sai ka zamto a dukkan halayenka akan haka!
Mazaje da yawa daga cikin mu akwai wadan da basu damu da me matayensu ke so ba, hakika yanda ake so matarka ta yi ma kwalliya da ado ita ma tana bukatar haka daga gareka, yana da kyau ma ka tambayi matarka kalar tufan da tafi son taganka da su domin ka rika yin irinsu kana dad'ad'a mata rai itama.
Yanda kake son magana mai dadi haka ita ma matarka take son magana mai dadi a koda yaushe
NA BIYAR KUMA: Gidan aure shine wurin sarautar 'ya mace, kuma a nan ne take ji a jikinta cewa tana zaman watayawa (da nade kafa) akan gadon mulkinta, kuma lallai ita jagora ce a cikin wannan gida, Ina gargadarka kan rushe mata masarautar da take rayuwa a cikinta, ko kuma ka yi kokarin angaje ta daga gadon mulkinta; in kuma ka aikata haka; to kayi husuma ne da ita ko fito-na-fito akan abin da take mulka, Babu wata adawa kuma da tafi tsanani fiye da ta mai mulkin da ake fito-na-fito da shi akan mulkinsa, koda kuwa a zahiri yana nunar da sabanin haka!.
Wasu daga Cikin mazajen mu na yanzu sun dauka cewa, sune ke da ikon tsara dokar cikin gida, babu shakkah wannan kuskure ne don haka don Allah mazaje mu kula, hakika mata ita ke da hakki mafi girma a cikin gidanta.
Sannan sai ya ci gaba da cewa:
NA SHIDA KUMA: Lallai mace tana son ta rabauta da samun mijinta, ba tare da kuma tayi hasarar iyalanta ba; don haka; Kada ka sanya kanka da danginta a ma'auni guda daya, har kace: Ta zabi ko kai, ko kuma danginta; saboda koda ta zabe ka akan danginta to ka sani; cewa zata wanzu ne cikin mummunan bakin-cikin da muninsa zai shigo rayuwarka ta yau da kullum!
Wasu daga Cikin Mazajen mu idan matayensu suka bukaci tafiya unguwa ko gayarda Iyaye sukan hana su, har ma wasu sukan ce ko fitar ko kuma ni, hakika wannan kuskurene mu kula don Allah.
NA BAKWAI KUMA: Lallai 'ya mace an halicce ta ne daga kashin-hakarkari karkatacce, kuma karkatar mace shine sirrin kyanta, haka kuma shine sirrin da ke jan maza zuwa gare ta
(har su fitinu da ita), wannan kuma ba aibi ba ne a gare ta, saboda gira (namarsa da gashinsa) ba komai ya kawata shi ba sai karkatarsa, don haka;
idan mace tayi kure kada ka tasa ta a gaba; ba tausasawa ko rangwantawa, da nufin kokarin mikar da karkatarta; in kayi haka, sai ka karya ta; wanda kuma karyatan shine sake ta (rabuwar aure), Kada kuma ka kyale ta sakaka –in ta yi kuskuren-sai karkatarta ta karu, har ta riga ta kangare; ta yadda ba zata zama da taushi ko taji maganarka daga baya ba; A'a dole ne koyaushe idan tayi
kuskure ka kasance tsakanin abubuwan nan guda biyu tare da ita.
NA TAKWAS KUMA: Lallai su mata a lokacin halittarsu an dabi'antar da su kan butulce ma abokin zama (miji), da kuma musanta kyawawan abubuwan da yayi; kai da za ka kyautata ma 'daya daga cikinsu na tsawon zamani, sannan kuma sai ka munana mata sau daya; sai tace: Da dai ban taba samun wani abun alheri ba a wurinka; don haka; kada wannan dabi'ar tata ta daukeka kan kyamarta gabadaya, ko kuma kaurace
mata; saboda in ka ki wannan dabi'ar to ai ka gamsu da wassu dabi'un nata!
.NA TARA KUMA: Lallai mace ta kan samu kanta a wassu lokutan cikin yanayi na raunin jiki, da kunci a rai, wanda kuma har Allah (SWT) a cikin wadannan hali (na haila da jinin haihuwa) ya dauke mata wassu daga cikin farillan da ya farlanta mata; ma'ana: ya dauke mata yin sallah gabadaya, tare da jinkirta mata lamarin azumi, har sai lafiyarta ta dawo mata, dabi'arta kuma ta daidaita, A don haka; kaima a cikin halin jinin hailarta ko na haihuwa sai ka yi koyi da Allah a lamarinta; ma'ana: kamar yadda Allah (SWT) ya dauke mata farillansa, kai kuma sai ka rangwanta mata cikin abubuwan da ka ke nema da kuma takaita yawa-yawan umurninka!
NA GOMA KUMA: Ka sani! Mace a wurinka kamar daurarren bawanka ne (ba fita sai da izininka…); sai ka tausaya ma rashin 'yancinta, zata zame maka mafi alherin abun jin dadi, kana kuma mafi alherin wanda ake tarayya da shi!! Aminci ya tabbata a gare ka.
Lallai wadannan wasiyyoyin idan har miji ya bi su sau-da-kafa wajen samar da su ga matarsa to lallai zata rayu da shi cikin nasara da aminci, kuma za ta kasance cikin matan da suka ci ribar aure da more masa tun daga nan duniya,
Insha Allahu a rubutu nagaba zan rubuta abubuwa goma (10) da ya kamata mata su sani a zaman takewar aure.
Allah ya azurta mu da kyawawan halayyan musulunci da zamu zama mafiya alherin maza ga matanmu, amin!