-
"Allah shi ya ƙagi halitta kuma ya wajabtawa kansa kula da sha'anin halittunsa, baya gyan-gyaɗi balle bacci, koda yaushe ganinsa yana biye da sha'anin bayinsa, kullum yana shi Allah yana cikin sha'aninsa na kula da lamuran bayinsa"
-
" A rayuwa kada ka taɓa yin tunanin cewa wani yana da tasiri game da rayuwarka ko mutuwarka, rayuwarka a hanun Allah take, haka nan mutuwarka ma a hannunsa take, shi ne yake raya wanda yaso kuma yake kashe wanda yaso, kada kayi shi-sh-shigi a cikin lamarin Allah ta'ala, kada kace wane shi ne zai rayu wane kuma shi ne zai mutu, lafiyarka ba ita ce take tabbatar maka da cewa ba za ka mutu yanzu ba, haka nan rashin lafiyarka ba ita ce take tabbatar maka da cewa yanzu zaka mutu ba, yo sau nawa mai lafiya ya mutu ba tare da wata lalura ba, kuma sau nawa mara lafiya ya warke daga cutar da ake yi masa tsammanin mutuwa a dalilinta"
-
"Babu abin da yafi ƙarfin Allah balle kuma ya gagareshi, shi ne yake iya kashe rayayye kuma ya tayar da matacce, shi ne wanda hisabi ga bayinsa a bayan mutuwarsu domin ya tabbatar musu da adalcinsa"